An Kama Wanda Ake Zargi da Kashe Tsohuwar Matarsa a Jigawa

0
11

Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Jigawa ta kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, mai shekaru 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa, Hadiza Sale, mai shekaru 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Yuli, 2025, lokacin da ake zargin ya kai mata hari da sanda yayin da take dawowa daga kasuwa da daddare.

Bayan kisan, wanda ake zargin ya ɓuya na tsawon fiye da makonni biyu, kafin daga bisani jami’an ‘yan sanda daga ofishin Aujara su kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani, bayan bincike da tura jami’an sirri da aka yi domin gano maboyarsa.

Kakakin rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin a sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here