Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa yawan ma’aikatan da ƙananan hukumominta ke da su ne ya sa ba za su iya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba a halin yanzu.
A cewar babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji, gwamnatin ta umarci shugabannin ƙananan hukumomi da su tsara matakan da za su kai ga aiwatar da sabon tsarin albashin.
A wata sanarwa da ya fitar, Modu ya ce sau da dama gwamnatin tarayya na tura fiye da Naira miliyan 700 zuwa asusun ƙananan hukumomin jihar, amma a hakikanin gaskiya ana bukatar kusan Naira miliyan 778 domin biyan albashin ma’aikata gaba ɗaya.
Ya ce, sabanin Jihar Kano da ke da ƙananan hukumomi 44 amma da ma’aikata kusan dubu 30,000, Jihar Borno na da ƙananan hukumomi 27 kacal amma ma’aikatan da yawansu ya kai dubu 90,000.
Gwamnatin ta ce tana ci gaba da nazarin hanyoyin da za a bi domin tabbatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashin ba tare da tabarbarewar tsarin albashi ba.