Rundunar Sojin ƙasar nan tayi watsi da wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna da cewa an kama wani dillalin makamai daya shigo Najeriya daga ƙasashen waje a kwanan nan.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon tsoho ne tun daga shekarar 2021, kuma ya shafi kama wani ɗan Nijar mai suna Shehu Ali Kachalla da ‘yan sanda suka yi a Zamfara.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta bayyana cewa Kachalla ya amsa cewa ya sayar da bindigogi fiye da 450 da harsasai ga ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara, Kaduna da Neja.
Rundunar ta ce yaɗa tsohon bidiyon wani yunkuri ne na yaɗa ƙarya da rage darajar kokarin jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci. Sojin sun bukaci jama’a da su yi watsi da bidiyon, tare da gargadin masu kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yada su.