Rashin hanyar ruwa na barazana ga wasu yankunan ƙaramar hukumar Albasu

0
17

Wasu daga cikin al’ummar Fanda a Hamdullahi, dake ƙaramar hukumar Albasu, sun koka game da matsalar rashin hanyar ruwa wadda ke haifar musu da zaizayar ƙasa.

Daya daga cikin Mazauna garin, mai suna Muhammad Salees, ya shaidawa Daily News 24 Hausa, cewa Zaizayar ƙasar na neman cinye makarantar Sakandaren Arabiyya, da kuma wata Firamare dake garin Hamdullahi, don haka suna neman mahukunta su kawo musu ɗauki, musamman yadda ake cikin yanayin damina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here