Jam’iyyar APC ta naɗa Ministan Harkokin Jinƙai da Ci gaban Al’umma, Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban ta na ƙasa.
An sanar da wannan naɗin ne a ranar Alhamis yayin taron kwamitin zartarwar APC na ƙasa (NEC) da aka gudanar a birnin Abuja. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda kuma ke jagorantar kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ne ya bayyana hakan.
Naɗin Nentawe ya samu amincewa ne bayan an gabatar da kudiri da kuma samun goyon bayan Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas. Nan take aka rantsar da shi a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Nentawe, ɗan asalin Jihar Filato, shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023.