Wani mummunan lamari ya faru a kauyen Jinkiri da ke ƙaramar hukumar Bauchi a ranar Talata da rana, inda matasa uku suka rasa rayukansu sakamakon nutsewa a wani kogi dake kusa da wurin hakar ma’adanai.
Wadanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da Habibu Mohammed da Abubakar Mohammed, dukkansu ‘yan shekara 16, da kuma Zailani Sule mai shekaru 14. Rahotonni sun bayyana cewa matasan sun je yankin tare da wasu samari domin neman tarkacen ma’adinai, kafin su shiga kogin domin yin wanka, daga nan kuma suka rasu.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu. Ta kuma jaddada bukatar wayar da kai kan hadurran da ke tattare da shiga koguna, musamman a lokutan da yanayi ya ke da hadari.