Manoman Masara Da Doya Sun Koka Kan Karancin Ruwan Sama

0
12

Manoma a yankin Kudu maso Kuduncin jihar Filato sun koka kan karancin ruwan sama da ke barazana ga amfanin gonarsu. Yankin ya kunshi ƙananan hukumomi shida da suka hada da Wase, Langtang Arewa da Kudu, Mikang, Shendam da Qua’an Pan.

Manoman sun ce kusan kwanaki 30 kenan babu isasshen ruwa, lamarin da ya sa amfanin gona irin su masara, gyada, wake da doya ke fara bushewa, kafin su kai ga girbi.

Yusuf Maidoki daga Shendam da Joseph Domle daga Langtang sun bayyana damuwarsu, suna mai fatan Allah ya kawo ruwa kafin lamarin ya kai ga babbar asara. Daniel Ishaku daga Qua’an Pan ya roki Allah ya kawo ruwa domin cigaban noman doyar da suke don tsoron tafka asara.

Idan za’a iya tunawa dai cibiyoyin hasashen yanayi sun sun yi gargadin cewa za a samu karancin ruwa a wasu yankuna na Najeriya daga ƙarshen Yuli zuwa farkon Agusta. Wannan matsalar dai ta jefa manoma cikin fargaba game da yawan girbi da kuma wadatar abinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here