Kotu ta tura mawaƙi Hamisu Breaker gidan gyaran hali

0
17

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da fitaccen mawaki, Hamisu Sa’id (Breaker), a gaban kotun tarayya da ke Dutse, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sale Musa Shuaibu, bisa zargin cin mutuncin takardar kuɗi ta Naira.

EFCC ta bayyana cewa an kama mawakin ne bayan ya watsa takardun kuɗin Naira ₦200 a wajen wani biki da aka gudanar a garin Hadejia, Jihar Jigawa, wanda jimillar kuɗin da aka watsar ya kai Naira dubu talatin.

Da aka karanto masa laifin sa a kotu, nan take ya amsa, sannan kotun ta yanke masa hukuncin daurin wata biyar a gidan yari ko kuma biyan tara ta Naira dubu ɗari biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here