Rahotonni sun bayyana cewa jami’an shige da fice sun kama Sanata Natasha, a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe, dake Abuja, yayin da take shirin tafiya ƙasar Birtaniya.
Lamarin ya faru a safiyar Alhamis a daidai lokacin da dakatacciyar Sanatar ke kokarin hawa jirgi domin tafiya tare da rakiyar mai gidanta.
Zuwa yanzu dai ba’a samu fitar wani dalilin kamen nata ba.