Gwamnatin Jigawa ta zaftare kaso 50 na farashin takin zamani

0
13

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya zaftare kaso 50 na farashin takin zamani don sauƙaƙawa manoma da kuma kokarin samar da abinci ga al’umma.

Shugaban ma’aikatan Gwamnan Jigawa kuma Shugaban Kwamitin Samar da Takin Zamani, a jihar Sanata Mustapha Makama, ya bayyana wasu sabbin matakai da zasu ɗauka game da rarraba takin bayan kammala taron kwamitin a Dutse, babban birnin Jigawa.

A cewarsa, za a sayar da buhun takin NPK a kan farashin Naira dubu 28 da dari 8, domin tallafa wa manoma da bunkasa harkar noma da samar da isasshen abinci a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Umar Namadi, ya yi gargaɗi ga dillalan takin zamani da wakilan al’umma da su guji fitar da takin zuwa wajen jihar, inda ya bayyana cewa duk wanda aka kama da irin wannan laifi, zai fuskanci hukunci.

Tsadar taki dai na ɗaya daga cikin matsalolin da manoma ke kokawa akai musamman a wannan shekara, wanda hakan yasa wasu manoma jingine noman shinkafa da masara sakamakon cewa suna bukatar taki mai yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here