EFCC Ta Kama Daliban BUK su 24 Bisa Zargin Aikata Zamba A Intanet

0
12

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta kama dalibai 24 daga Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) bisa zargin su da aikata zambar kuɗaɗe ta intanet.

An kama waɗanda ake zargin ne a ranar Litinin yayin wani samame na bazata da jami’an hukumar daga ofishin EFCC na shiyyar Kano suka gudanar.

Kamen ya biyo bayan makonni jami’an na tattara bayanan sirri da sanya idanu, akan ɗaliban wanda ya nuna alamar cewa waɗanda ake zargin suna da alaka da damfara ta yanar gizo, satar bayanan mutum, da kuma yaudarar mutane a sace musu kuɗi ta hanyar amfani da fasaha.

A lokacin samamen, jami’an EFCC sun kwato kwamfutocin tafi-da-gidanka, wayoyin hannu, na’urorin intanet (routers), da kuma mota kirar Honda Accord daga hannun waɗanda ake zargin.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Ismail Nura, Suuleyman Ayeh, da Usman Abdulrazaq, tare da wasu da dama. Hukumar ta ce bincike na ci gaba da gudana, kuma za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala.

Wannan samame na baya-bayan nan ya zo ne kwana kalilan bayan wani irin sa da aka yi a ranar 17 ga Yuli, inda EFCC ta cafke mutum 23 da ake zargi da zamba ta yanar gizo a wani wuri da ke kan hanyar Kano-Zaria.

 Hukumar ta bayyana cewa wurin yana da alaka da horar da masu damfara ta intanet, inda aka kwato wayoyi 12, kwamfutoci 2 da wasu takardun shaidu masu tabbatar da laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here