Al’ummar Zamfara Sunyi Zanga-Zanga kan Ƙaruwar Hare-Haren Ƴan Bindiga

0
13

Wasu mazauna ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka nemi daukin gaggawa daga gwamnati kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga a yankin.

Masu zanga-zangar sun ce an kashe fiye da mutum 100 a kauyuka da dama ciki har da Mada, Ruwan Bore, da Fegin Mahe, yayin da gonaki da shaguna suka lalace sakamakon rashin tsaro. Wani daga cikin masu zanga-zangar mai suna, Malam Abubakar Abdullahi, ya ce an sace masa kayayyaki da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan ɗaya sakamakon ayyukan rashin tsaro.

Shugaban ƙaramar hukumar Gusau ya ce gwamnati na aiki da hukumomin tsaro don shawo kan matsalar, tare da shirin tura jami’an tsaro zuwa wuraren da abin ya fi shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here