Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta gano wata ma’ajiya a Jihar Kano da ke ƙunshe da fiye da lita 88,000 na sinadarai masu haɗari, masu suna Nitric acid da Sulphuric acid, waɗanda ake amfani da su wajen haɗa abubuwan fashewa.
Jami’an hukumomin sun bayyana cewa irin wadannan sinadarai ana iya amfani da su wajen kera abubuwan fashewa masu haɗari.
NAFDAC ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa sintiri da aiwatar da dokokinta a duk fadin Najeriya, musamman a yankin Arewa, domin dakile yaduwar miyagun ƙwayoyi da sinadarai masu hadari.
Hukumar ta kuma bukaci al’umma da su rika sanar da duk wani motsi ko aiki da suke zargi a cikin unguwanninsu domin taimakawa wajen kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaro.
A wani samame na daban, hukumar NAFDAC tare da haɗin gwiwar hukumar hana fasa kwauri , reshen Kano da Jigawa, sun lalata muggan ƙwayoyin Tramadol guda 491,000 na Tramadol, wanda darajar kuɗin su ta kai naira miliyan 91.