Majalisar wakilai na neman hana ma’aikatan gwamnati saka yaran su a makarantu da asibitocin kudi

0
9

Majalisar Wakilai na neman kawo ƙarshen yadda ma’aikatan gwamnati da ’ya’yansu ke dogaro da makarantun kudi da kuma asibitocin kudi domin samun ilimi da lafiya.

Wannan na zuwa ne bayan gabatar da wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Isuikwuato/Umunneochi ta jihar Abia, Amobi Ogah, ya yi a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Talata.

Yayin ganawa da manema labarai, Ogah ya bayyana cewa kudirin dokar na da nufin dawo da kwarin gwiwa da amana a fannin ilimi da lafiya na gwamnati a Najeriya.

“A gaskiya wannan kudiri wani muhimmin sauyi ne ga ƙasarmu, dole ne mu tilasta wa jami’an gwamnati su tsaya su gyara cibiyoyin da suke jagoranta, maimakon su guje musu zuwa na kudi,” in ji shi.

Ya kawo misali da shahararrun shugabannin Najeriya na farko kamar Sir Ahmadu Bello, Dr. Nnamdi Azikiwe, Chief Obafemi Awolowo da Sir Abubakar Tafawa Balewa, wadanda duk sun halarci makarantun gwamnati ko na mishan, amma suka fito a matsayin manyan shugabanni masu hangen nesa.

Ogah ya kara da cewa yawan fifita makarantun kudi da asibitoci masu zaman kansu da jami’an gwamnati ke yi na kara jefa ayyukan gwamnati cikin rauni da koma baya.

Haka kuma, ya soki yawan kudin da Najeriya ke yin asara ta hanyar yawon neman lafiya da ilimi a ƙasashen waje, yana mai cewa a zamanin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari na shekaru takwas, ƴan Najeriya sun kashe akalla dala biliyan 29.29 wajen yin jinya a kasashen waje kadai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here