Majalisar dattawa ta nemi gwamnatin tarayya ta saka sunan Alhaji Aminu Dantata a wani muhimmin waje
Majalisar Dattawan ta nuna wata girmamawa ga Alhaji Aminu Dantata bisa gudunmuwar da ya bayar wajen taimakon al’umma da ci gaban ƙasa.
Wannan mataki ya biyo bayan wani kuduri da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da hadin gwiwar Sanata Rufa’i Hanga da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila suka gabatar a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Talata.
Yayin gabatar da kudirin, Sanata Barau ya bayyana Alhaji Aminu Dantata a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa, wanda ya sadaukar da dukiyarsa da lokacin rayuwar sa domin taimaka wa jama’a tare da neman yardar Allah.