Majalisar dattawa ta amince da bukatar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar ta neman aron kuɗi daga ƙasashen waje da ya kai sama da dala biliyan 21, da kuma ƙarin dala biliyan 2 daga cikin gida, domin aiwatar da muhimman ayyuka daga shekarar 2025 zuwa 2026.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin bashi na cikin gida da na waje da shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko, ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da ayyuka a fannonin gine-gine, noma, tsaro, wutar lantarki da kuma fasahar sadarwa.
Cikin shirin, an ware dala biliyan 3 domin farfaɗo da layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
Sanatoci da dama sun nuna goyon bayansu ga wannan shiri, suna masu cewa wannan mataki zai tabbatar da adalci ga dukkan yankunan ƙasar nan, tare da kasancewa cikin tsarin da ƙasashen duniya ke bi domin habaka tattalin arzikin su.