Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), sun gudanar da taron wayar da kai kan illolin shaye-shaye a cikin al’umma, musamman tsakanin direbobi da matasa masu yawan mu’amala da tituna.
An gudanar da taron ne a babban ofishin KAROTA da ke titin Club Road, inda wakilan NDLEA suka gabatar da bayani dalla kan yadda shan miyagun kwayoyi ke barazana ga tsaron hanyoyi da lafiyar jama’a.
Shugaban KAROTA, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya ce taron na cikin sabbin matakan da hukumar ke ɗauka domin inganta tsaro da tarbiyya a kan tituna, yana mai jaddada cewa shaye-shaye na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hadurra da rikice-rikicen zamantakewa.
“Wannan taro ba zai tsaya a nan ba, muna da shirin ci gaba da wayar da kai a ciki da wajen hukumar. Bugu da ƙari, za mu shirya horo na mako guda tare da NDLEA don faɗakar da ma’aikatanmu,” in ji shi.
A cewarsa, horon zai kunshi hanyoyin gano masu shaye-shaye, dabarun yaki da fataucin kwayoyi, da kuma yadda za a kare kai daga hatsarin da ke tattare da su.
NDLEA ta yaba da wannan mataki na KAROTA, tana mai bayyana cewa haɗin kai irin wannan na da muhimmanci wajen ganin an samu zaman lafiya da tsaro a fadin Jihar Kano.