Hukumar kula da ayyukan ƴan sanda zata yi ƙarin girma ga jami’ai 4,741

0
20

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta amince da ƙarin girma ga jami’an ‘yan sanda 4,741 bayan kammala ganawar kwamitin tantance jami’ai da aka gudanar a faɗin ƙasa kwanan nan.

Daga cikin waɗanda aka ɗaga matsayinsu, mutum 4,708 ne aka bawa matsayin ASP da ba a tabbatar ba, yayin da 33 suka samu karin girma zuwa SP.

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa hukumar ta kuma amince da ƙarin girma ga jami’ai 38 daga cikin kwararrun DSP zuwa matsayin SP, sannan 29 daga cikin Sufeta na musamman zuwa matsayin CSP.

Wannan na daga cikin abubuwan da aka tattauna a taron hukumar da aka kammala a birnin Abuja, ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

Hukumar ta kuma amince da karin girma ga kwamishinonin ‘yan sanda 12 zuwa matsayin AIG, kwamishinoni 16 zuwa matsayin cikakken matsayin kwamishina, da kuma mataimakan kwamishinoni 28 zuwa matsayin kwamishinoni.

Shugaban hukumar, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya) ne ya jagoranci zaman, tare da halartar Hon. Justice Paul Adamu Galumje (mai ritaya), wakilin bangaren shari’a a hukumar; DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya), wakilin rundunar ‘yan sanda; da kuma Hon. Justice Christine Ladi Dabup (mai ritaya), wakiliyar kotunan jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here