Gwamnatin Kano zata ɗauki nauyin ƙaro karatun likitoci a ƙasar waje

0
10

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da wani shirin horo na musamman a matakin digiri na biyu a ƙasashen waje, wanda aka tanadar domin likitoci da ma’aikatan jinya da ke da ƙwarewa a wasu fannoni na kiwon lafiya.

Shirin zai mai da hankali ne kan muhimman fannonin kula da marasa lafiya da ke da ƙarancin ƙwararru a jihar Kano.

A cewar wata sanarwa da Dr. Mansur Mudi Nagoda, Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ya fitar, wannan tallafin zai shafi fannonin lafiya guda 19 da suka haɗa da:

Cutar fata, Cutar koda, Kulawar ta musamman, Wankin ƙoda, Dashen ƙoda, Tiyatar ƙananun yara, Maganin tabin hankali, Kula da kunne, hanci da makogwaro, Maganin ciwon zuciya, Gyaran ƙashi, Fasahar binciko cutuka ta hanyar amfani na’urar hoto, Aikin gyaran fata, Kula da masu cutar daji, da sauran su.

Dr. Nagoda ya bayyana cewa wannan wata babbar dama ce ga ma’aikatan mu na lafiya domin samun sabbin ilimi da ƙwarewar zamani wanda zai taimaka matuƙa wajen inganta kula da marasa lafiya a jihar Kano. Mun fi mai da hankali kan fannonin da ake da ƙarancin ƙwararru a halin yanzu.”

Ana buƙatar wanda ke sha’awar shiga shirin ya kasance yana da digiri na farko (BSc) a fannin lafiya.

Masu sha’awa za su rubuta takardar neman gurbin zuwa ga Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci, tare da haɗa takardun shaida da sauran muhimman bayanai da suka dace.

Ana buƙatar a mika dukkan takardun neman gurbin kafin ranar Litinin, 28 ga Yuli, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here