Gwamnatin  Kano ta sanar da lokacin hutun makarantun Boko

0
7

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025 ne lokacin da za’a fara hutun zangon karatu na uku a dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu wadanda ke koyar da karatun firamare da na sakandare, ciki har da na kwana.

A wata sanarwa da Balarabe Abdullahi Kiru, Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ya fitar, an shawarci iyaye da masu kula da ɗaliban makarantu na kwana da su shirya tsaf domin dawo da ‘ya’yansu gida tun a safiyar ranar hutun.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ɗaliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, yayin da ɗaliban makarantun rana za su koma ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ya ja hankalin iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da yin biyayya ga ranar komawa makaranta kamar yadda aka tsara. Ya ce duk ɗalibin da ya ƙi bin wannan umarni zai fuskanci hukunci.

Dr. Makoda ya kuma bayyana godiyarsa ga iyaye da al’ummar jihar bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa ma’aikatar. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here