Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan gaba na Ingila, Marcus Rashford, daga Manchester United a matsayin aro har zuwa ranar 30 ga Yunin shekarar 2026.
Rahotanni sun bayyana cewa zakarun na LaLiga suna da damar siyan ɗan wasan gaba ɗaya bayan kammala yarjejeniyar aron.
Rashford ya amince da rage albashinsa domin sauƙaƙa komawarsa Camp Nou, alamar cewa yana da kwadayin gasar Sifaniya.