Manoman shinkafa da masara a sassa daban-daban na Najeriya na fuskantar barazanar tafka asarar noma, sakamakon hauhawar farashin taki da sauran kayan aikin gona.
Wasu daga cikin manoman ma sun hakura da ci gaba da noman shinkafa, inda suka juya zuwa noman wasu amfanin gona kamar gero, dawa, rogo da riɗi, saboda ganin cewa tsadar taki ba za ta bar su su ci riba ba.
Wannan na faruwa ne duk da iƙirarin gwamnatin tarayya na cewa ta rage farashin takin zamani don sauƙaƙa wa manoma domin bunkasa harkokin noma.
Wani manomi daga jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Idris, ya shaida wa BBC cewa ya kashe naira miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas wajen siyan taki da kuma kashe kuɗin ban ruwa a kowace kadada.
“Duk kuɗin da na kashe, gaskiyar magana babu wani riba da zan samu, idan ka dubi farashin taki da yadda ake sayar da buhun shinkafa a yanzu, lamarin bana ƙarfafa gwuiwa bane,” in ji shi.
A cewarsa, a kalla buhu 40 zuwa 60 ake iya samu daga noma a kowace hecta, amma idan aka ƙididdige farashin taki da sauran hidima, sai a ga babu abin da ya rage da za’a samu a matsayin riba.
Rahotanni na nuna cewa manoma da dama sun sauya daga noman shinkafa da masara zuwa wasu amfanin gona da ke buƙatar kuɗi kaɗan wajen kula da su.
Alhaji Idris ya yi kira ga gwamnati da ta sake nazari kan harkar noma, tare da saka tallafi a farashin taki da kuma samar da magungunan kashe ciyawa a farashi mai rahusa domin rage wa manoma wahala.