Sarkin Daura ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a 2027, saboda ya karrama Buhari

0
8

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Daura yayin da yake karɓar bakuncin uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da wasu matan gwamnoni daga sassan ƙasar nan, wadanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

A yayin ziyarar, Sarkin Daura ya yaba da yadda Shugaba Tinubu ya nuna girmamawa da mutuntawa ga marigayi Buhari, musamman a lokacin jana’izarsa, yana mai cewa hakan ya nuna irin halin dattako da shugabanci na adalci da Tinubu ke da shi.

A cewar rahoton Premium Times, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ne ya jagoranci tawagar zuwa Daura domin isar da saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Buhari.

Sarkin ya kara da cewa irin wannan kima da daraja da Shugaba Tinubu ya nuna, ya tabbatar da cancantarsa wajen ci gaba da jagorantar ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here