Wani jigo a jam’iyyar APC, Chief Sam Onuigbo, ya bayyana cewa mutuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba za ta shafi damar samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Ya kuma ce karfin da jam’iyyar ADC ke samu sakamakon sauyin sheƙar wasu fitattun ‘yan siyasa ba barazana ba ce ga APC ba, yana mai cewa manufofin gwamnatin Tinubu na cigaba da samun karɓuwa a wajen jama’a.
Onuigbo ya ƙara da cewa APC ba jam’iyya ce da aka gina kan Buhari kaɗai ba, sai dai an gina ta domin demokraɗiyyar Najeriya ta kai matakin da ake fifita manufofi fiye da mutum ɗaya.