Mambobin ISWAP sun kashe ƴan-sa-kai da mafarauta a Borno

0
11

Mambobin kungiyar ISWAP sun kashe mutane bakwai da suka haɗa ‘yan sa-kai da mafarauta a karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno.

A cikin wani bidiyo mai tsawon minti 6 da daƙiƙa 41 da jaridar Daily Trust ta samu, an ga wani ɗan ISWAP day rufe fuskarsa yana yi wa waɗanda aka kama tambayoyi ɗaya bayan ɗaya kafin a kashe su.

Bidiyon ya nuna mutanen da aka kama sanye da jajayen kaya a durƙushe, yayin da wasu mayakan ISWAP masu bindiga da wuka suke tsaye a bayansu.

Ɗaya daga cikin jagororin ISWAP ya zargi mutanen da cewa munafukai ne kuma suna haɗin guiwa da waɗanda ba musulmai ba, lamarin da yace sun cancanci a kashe su.

Daga nan ne bidiyon ya ci gaba da nuna yadda mayakan suka sare datse wuyan kowane ɗaya daga cikin mutanen da wuka, kafin a jefar da gawarwakin a wani rami.

Wani babban jami’i na karamar hukumar Magumeri wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa huɗu daga cikin waɗanda aka kashe ‘yan sa kai ne, da kuma mafarauta daga cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here