Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta bayar da umarnin wucin-gadi na hana Hukumar EFCC kamawa ko tsangamar Rabiu Tijjani, wani ɗan kasuwa da ke zaune a Dubai, bisa zargin da aikata damfarar dala miliyan $1.9.
EFCC ta bayyana Tijjani a matsayin wanda take nema, bisa wancan zargi, sai dai ya musanta zargin, yana mai cewa hakan kokarin ɓata masa suna ne, da barazana ga aikin matatar mai da yake yi.
Tijjani ya bayyana cewa ya shiga yarjejeniya da wani ɗan kasuwa, Ifeanyi Ezeokoli, kan musayar dala miliyan 76, inda daga baya aka samu matsala a lissafi.
Bayan ƙoƙarin sasanci ya ci tura, Tijjani ya kai ƙara DSS, amma Ezeokoli ya garzaya EFCC.
Kotun ta ce ba a tuntuɓi Tijjani kafin fitar da sanarwar neman sa ba, kuma hakan na iya ƙara cutar da shi.
Zuwa yanzu an dage sauraron ƙarar zuwa 18 ga Satumba.