Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Jihar Kano, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya bayyana cewa jami’ar ta yanke shawarar karrama marigayi Sheikh Ahmad Bamba sakamakon gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jami’ar tun kafin rasuwarsa.
Farfesa Kurawa ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da Premier Radio, inda ya ce wannan karramawa wata alama ce ta girmamawa ga marigayin bisa irin rawar da ya taka.
Taron karramawar zai gudana ne a ranar Asabar, 26 ga watan Yuli, a sabon dakin taro na Convocation Arena da ke cikin harabar jami’ar.
Sauran fitattun mutanen da za a karrama sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, Hajiya Mariya Sunusi Ɗantata, da kuma wasu mutane biyu.