Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwanaki uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga watan Yuli, 2025, inda ta yi hasashen yiwuwar saukar ruwan sama mai yawa da kuma iska mai ƙarfi a wasu sassan Najeriya.
A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, NiMET ta shawarci al’umma su dauki matakan kariya da taka-tsantsan, musamman a wuraren da ke da haɗarin ambaliya da ɓarnar da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.
Hukumar ta ce za a fuskanci canjin yanayi a jihohin Arewa, Kudu da kuma Yankin tsakiyar ƙasar nan, inda ake sa ran iska mai ƙarfi za ta haɗu da ruwan sama a lokuta daban-daban.
Hasashen yace a ranar litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba, Adamawa, Kebbi, Borno, Yobe, Gombe, Bauchi, Sokoto da Kaduna.
Haka kuma, jihohin Abuja, Niger, Plateau, Nasarawa, Benue da Kogi da ke cikin Yankin tsakiyar ƙasar nan, za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.
Talata da safe, ana sa ran ruwan sama zai sauka a Abuja, Kwara, Niger da Plateau, kuma zai ci gaba da sauka har zuwa tsakar rana.
Laraba da safe, za a samu iska mai ƙarfi da ruwan sama a jihohin Katsina, Kano, Bauchi, Sokoto da Taraba, sannan daga bisani ya bazu zuwa Yobe, Jigawa, Kaduna, Borno da Kebbi.
NiMET ta bukaci jama’a da su sanya ido, su bi ka’idojin kariya daga hadurran da irin wannan yanayi ka iya haifarwa, tare da haɗa gwuiwa da hukumomin da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.