Sowore Ya Zargi Ɗan Sanda da Sace Masa Gilashi a Lokacin Zanga-Zanga

0
8

Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya zargi wani ɗan sanda da sace masa gilashin ido mai ɗauke da na’urar tattara bayanai, a yayin wata zanga-zanga da aka gudanar a birnin tarayya Abuja a yau Litinin.

Zanga-zangar wacce Sowore ya jagoranta tare da wasu masu fafutuka da tsoffin jami’an ‘yan sanda, na neman a inganta walwalar jami’an tsaro da kuma fitar da tsoffin jami’an ƴan sandan daga tsarin fansho na haɗaka.

A cewar Sowore, jami’in da ake zargi wanda ke cikin fararen kaya an kama shi a wani bidiyon da ya nuna yadda ya sace gilashin na AI Rayban. 

Sowore ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here