Jahili ne kawai zai riƙa dukan matar sa–Sarki Sanusi II

0
9

Mai Martaba Sarkin Kano, na 16 Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata cin zarafin mata da yara a Jihar Kano, yana mai jaddada cewa babu wani Musulmi nagari da ke dukan matarsa.

Sarkin ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun karuwar aikata fyade da kuma dukan mata a tsakanin ma’aurata, yana mai cewa malamai da limamai suna da rawar takawa wajen canza halayen jama’a domin kawo ƙarshen wannan mummunar dabi’a.

Sanusi ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi tawagar cibiyar cigaban harkokin bincike da nazari ta (dRPC) tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Al’adu da Fahimtar Juna ta Jami’ar Bayero Kano (CICID) a fadarsa da ke Kano.

Tawagar ta kai ziyarar ne a wani bangare na yaɗa manufofinta wajen horar da shugabannin Musulmai domin su taka rawa wajen yaƙi da cin zarafin mata a jihohin Arewacin Najeriya da Musulunci ya fi rinjaye. An samu tallafin wannan shiri ne daga gidauniyar Ford.

A cewar Sarkin, ni ban taɓa yarda da dukan mata ba, kuma masu aikata hakan ba wai gyara mata suke son yi ba, illa cutar da mata. 

Muslinci ya ɗaukaka matsayin mace fiye da kowane addini, amma waɗanda ke cin zarafin mata suna amfani da addinin ne ba da ilimi ba. Wanda ke dukan matarsa bai cancanci kiransa da mutumin kirki ba. Wannan ba magana ta ba ce, Annabi Muhammadu (SAW) ne ya faɗa. Sai marasa karatu ko jahilci ne hakan ne ke yin haka, inji Sarkin.

A nasa jawabin, Daraktan CICID, Dr. Taofeek Abubakar Hussain, ya shaida wa Sarkin cewa aikin su ya ya horar da alkalai na kotunan Shari’a da malamai kan yadda za su warware shari’o’in da suka shafi cin zarafin mata da sauƙi kuma cikin adalci.

Dr. Hussain ya kuma roƙi Sarkin da ya duba yiwuwar komawa kan tsarin dokar iyali ta Musulunci da aka fara duba ta a baya, tare da ba su dama su horar da masu rike da sarautun gargajiya a masarautar kan irin rawar da za su taka wajen yaƙi da wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here