Hukumar kula da ayyukan shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta sauke Adamu Salisu daga mukaminsa na maga takardan babbar Kotun jiha mai lamba 13, bisa samunsa da laifin fitar da jabun takardun shaidar sammaci da kuma sa hannu a takardun da ba shi da hurumi.
Sanarwar da mai magana da yawun hukumar shari’a ta jihar, Baba Jibo-Ibrahim, ya fitar ta bayyana cewa Salisu ya amsa laifinsa, wanda ya sabawa ƙa’idojin aikin shari’a.
Hukumar ta JSC ta rage masa matsayi daga matakin aiki na 13 zuwa 12 tare da yi masa gargaɗi mai tsanani kan sake aikata irin wannan laifi.
Haka kuma, wani ma’aikaci, Yusuf Ayuba, ya samu hukunci na sauke shi daga matakin aiki na 5 zuwa 4 bayan an same shi da laifin dena zuwa aiki na tsawon wata huɗu ba tare da izini ba.
Hukumar ta ce wadannan matakai na ladabtarwa na da nufin dakile halayen rashin ɗa’a da ƙarfafa gaskiya da bin doka a ɓangaren aikin shari’a.