Gwamnan Kano Ya Ƙaddamar da Tallafin Sana’o’i ga Matasa 1,130

0
13

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da shirin tallafawa matasa 1,130 da suka kammala samun horaswa daga cibiyoyin koyon sana’o’i guda shida da aka farfado da su a jihar.

Sakataren kwamitin kula da cibiyoyin horar da sana’o’i guda 26 a jihar, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ne ya bayyana haka a karshen mako yayin taron tattaunawa da masu ƙananan sana’o’i a sashin koyar da harkokin Kasuwanci ta Dangote, dake Jami’ar Bayero, Kano.

 Wannan mataki yana daga cikin kokarinsa na rage rashin aikin yi da kuma farfaɗo da sana’o’in dogaro da kai.

 Masu amfanar tallafin sun samu horo a fannonin kiwon dabbobi, noma, fasahar kwamfuta, fim, da kiwon kifi. 

Haka zalika, wasu matasa da aka ceto daga shan miyagun ƙwayoyi suna daga cikin wadanda za’a bawa tallafin.

 Tallafin ya haɗa da ba su kayayyakin aikin sana’a da kuɗaɗen farawa.

A lokaci guda, gwamnatin ta shirya buɗe ƙarin cibiyoyi guda biyar da za su ɗauki matasa 1,600, ciki har da mata 600 da za su koyar da kiwon kaji, da cibiyoyin gyaran hali, jarida da wasanni. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here