Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa gwamnan jihar, Dikko Umar Radda, na cikin koshin lafiya bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Maiwada Dammallam, hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota ƙirar Golf ta kauce hanya, ta bugi motar da gwamnan ke ciki a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Daura.
Maiwada ya shaida wa BBC cewa an garzaya da gwamnan da sauran mutanen da ke cikin motar zuwa asibitin Daura domin ba su taimakon gaggawa. Daga bisani kuma, an mayar da gwamnan zuwa Asibitin Koyarwa na Katsina, inda ƙwararrun likitoci suka tabbatar da cewa lafiyarsa kalau.
Ya kuma bayyana cewa akwai mutum uku a cikin motar tare da gwamnan lokacin da hatsarin ya faru, su ne shugaban ma’aikatan gwamna, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; Hakimin Kuraye; da kuma Alhaji Shamsu Funtua. Dukkansu na cikin koshin lafiya, sai mutum ɗaya da aka yi masa dinki kadan.
Wannan bayani ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa gwamnan ya samu mummunan rauni.