An gudanar da addu’o’i na musamman domin girmama tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, a Babbar Cocin Ƙasa (National Christian Ecumenical Centre), da ke Abuja a ranar Lahadi.
An shirya wannan taro ne domin nuna karramawa ga rayuwar marigayin, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Landan yana da shekaru 82.