Fiye da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon ambaliya a garin Zakirai, dake karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano, bayan ruwan sama mai ƙarfi ya sauka a yankin.
Ambaliyar ta kuma lalata wani ɓangare na layin dogo da kasuwar garin, lamarin da ake dangantawa da ginin magudanan ruwa marasa inganci a cikin aikin titin kilomita biyar da ke gudana a yankin.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ruwa yana ci gaba da shiga gidajensu, inda wasu suka bar muhallansu, yayin da wasu ke zaune a cikin ruwa.
Ruwan ya lalata duk abincin da muka tanada, muna neman agajin gaggawa daga gwamnati da masu hannu da shuni,” in ji wata mazauniyar garin, Sa’adatu.

Masana sun ce Zakirai ba ta da tarihin afkuwar ambaliyar ruwa, amma aikin ginin titin ne ya haddasa wannan matsala a wannan lokaci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce aikin titin na daga cikin shirye-shiryen da aka fara a lokacin mulkin Sanata Rabi’u Kwankwaso don inganta yankunan karkara, amma gwamnati ta baya ta dakatar da su.
A baya-bayan nan, gwamnan ya soke irin wannan kwangila a ƙaramar hukumar Garko saboda rashin fara aikin lokacin da ya kamata.