Jagorar jam’iyyar Conservative ta ƙasar Birtaniya, Kemi Badenoch, ta bayyana cewa samun takardar zama ɗan ƙasar Birtaniya zai ƙara yin wahala ga ’yan Najeriya muddin har ita ce ke kan karagar jagorancin ƙasar.
A wata hira da aka yi da ita a tashar CNN a ranar Lahadi, Badenoch ta ce akwai buƙatar a sake fasalin tsarin shige da ficen ƙasar Birtaniya, inda ta kwatanta dokokin shige da ficen Najeriya da na Birtaniya.
Akwai ’yan Najeriya da dama da ke zuwa Birtaniya su zauna, daga baya kuma su mallaki shaidar zama ƴan ƙasar, ya kamata mu daina yin sakaci da hakan,” in ji ta.
Karkashin jagorancina, mun fito da sabbin manufofi da za su sa samun shaidar zama ɗan ƙasar Birtaniya ya ƙara wuya, saboda abin ya yi sauƙi fiye da yadda ya kamata ya kasance, a cewar ta.
Badenoch ta bayyana cewa tsarin da ake da shi yanzu yana da rauni, kuma ana iya amfani da shi ta hanyoyi marasa kyau da za su iya kawo barazana ga tsaron Birtaniya.
A lokacin da aka tambaye ta game da ra’ayinta kan yadda wasu ’yan Najeriya ke ƙoƙarin kafa wata karamar ƙasar su a cikin Burtaniya, domin inganta hadin kai tsakanin su, da kuma kwaikwayon rayuwar Burtaniya, Kemi ta ƙalubalanci hakan.
Mutane da dama na zuwa ƙasarmu su aikata abubuwan da da ba za su taɓa amincewa da su a ƙasashensu ba, Kemi ta ƙara da cewa.
Duk da cewa Kemi Badenoch tana da takardar shaidar zama ƴar asalin Najeriya, amman an haife ta a Birtaniya, daga ga iyayen ta ’yan Najeriya, kuma ta yi wani ɓangare na ƙuruciyarta a Najeriya.
Sai dai kalamanta sun jawo ce-ce-ku-ce a ƙasashen biyu.
Wasu na ganin tana ƙara nuna tsattsauran ra’ayi kan batun shige da fice da kuma yadda take nisanta kanta daga tushenta na asali wato Najeriya.