Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kamu da ciwon kumburin hanji wanda ya sa likitoci suka shawarce shi da ya huta na tsawon kwanaki uku.
A cewar wata sanarwa daga ofishinsa a ranar Lahadi, an gano cewa Netanyahu, mai shekara 75, yana fama da ciwon kumburin hanji da kuma rashin ruwa a jikinsa. Sanarwar ta ce yanzu haka yana karɓar magani ta hanyar ƙarin ruwa, kuma yana samun sauƙi.
Netanyahu, wanda aka saka wa na’urar taimaka wa bugun zuciya a shekarar 2023, an kuma yi masa tiyatar mafitsara a watan Disambar bara.
A halin yanzu, an bayyana cewa firaministan zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida yayin da yake hutawa.
Tashar Channel 12 ta ruwaito cewa ba zai halarci zaman majalisar dokokin ƙasar (Knesset) na ranar Lahadi ba, kana kuma zaman shari’arsa da aka shirya a Kotun Gundumar Tel Aviv zai gudana a ranar Litinin.