Farooq Kperogi Ya Nemi Gafarar Aisha Buhari Kan Zargin Rabuwa da Buhari

0
6

Farooq Kperogi, malamin aikin jarida da ke zaune a Amurka, ya nemi afuwa daga Uwargidan tsohon shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, kan wani rubutun da ya wallafa a Facebook inda ya yi zargin cewa ta rabu da marigayi Muhammadu Buhari, kafin rasuwar sa.

Kperogi ya bayyana cewa ya samo bayanin sakin ne daga wata majiya mai aminci.

Ya ce fitar da bayanin ya jawo damuwa ga Aisha Buhari da mutanenta, kuma hakan ya saba da ƙa’idojin aikin jarida.

Tsohon mai taimaka wa Aisha Buhari, Alhaji Sani Zorro, ya musanta zargin tare da bayyana cewa aurenta da Buhari yana nan daram kafin mutuwarsa.

Kperogi ya amince cewa ita kaɗai ce ke da ikon bayyana halin da aurenta ke ciki, kuma ya nemi gafararta bisa wannan kuskure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here