ASUU Ta Yi Fatali Da Sauya Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Sunan Buhari

0
6

Ƙungiyar Malaman Jami’a ta ƙasa (ASUU) reshen Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta bayyana ƙin amincewarta da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na sauya sunan jami’ar zuwa na tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Shugaban ƙungiyar, Dr. Abubakar Mshelia Saidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce wannan yunkuri siyasa ne kuma abin kunya ne ga tarihin jami’ar da mutuncin ilimin da take dashi tun lokacin kafuwarta zuwa yau.

An sanar da wannan canjin suna ne a wani taron musamman na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da aka gudanar a ranar 17 ga Yuli domin karrama marigayi Buhari, amma hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ciki da wajen jami’ar.

ASUU ta ce yanzu haka tana shirin haɗa tawagar wakilai, dattijai da shugabannin ƙungiyar domin dakile wannan yunkuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here