Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da gangogin su ta ƙasa ICPC ta shirya gurfanar da Shugaban zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da wasu jami’ai biyu a kotu a ranar 21 ga Yuli, 2025, kan zargin karkatar da naira biliyan 1.02.
Binciken ya nuna cewa an fitar da kuɗin daga asusun KANSIEC zuwa wani kamfani da ba shi da alaƙa da hukumar.
Duk da cewa jami’an hukumar sun ce kuɗin na biyan ma’aikatan wucin gadi ne, ICPC ta ce bata amince da bayanin hakan ba.
Haka kuma, akwai zargin karkatar da naira miliyan 20 da aka ce an ware don tantance ‘yan takara, amma ICPC ta gano cewa tantancewar an yi ta ne a hedikwatar hukumar kawai, ba a fadin jihar Kano ba.