Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai halarci ziyarar ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kano ba, saboda ya tafi London domin wata harka ta kansa, inji tsohon Shugaban Ma’aikatansa, Malam Muhammad Garba ya bayyana.
Garba ya ce tafiyar ba ta da alaƙa da rashin lafiya ko ficewa daga harkokin siyasa, domin an shirya ta tun bayan murabus ɗinsa daga shugabancin jam’iyya. Duk da ƙoƙarinsa na sauya tafiyar, hakan bai yiwu ba.
Ya ƙara da cewa Ganduje na ci gaba da mu’amala da shugabannin APC a Kano yayin ziyarar, kuma babu wata matsala tsakaninsa da Shugaba Tinubu. Haka kuma, jam’iyyar APC a Kano na nan cikin haɗin kai da biyayya ga shugabancin Tinubu.