Gwamnatin Tarayya ta ƙara adadin kuɗin da take kashewa a matsayin tallafi na wutar lantarki daga Naira biliyan 610 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 1.94 a 2024, kamar yadda rahoton jaridar The PUNCH ya bayyana.
Wannan ya nuna karin kaso 219.67 cikin ɗari na yawan kuɗin tallafi duk shekara, duk da ƙarin farashin wuta da akayi a tsarin shan wuta na Band A da aka aiwatar a watan Afrilu 2024.
Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC) tare da wasu masana sun bayyana cewa wannan ƙarin tallafin ya faru ne bayan karya darajar Naira da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Yuni 2024 da kuma cire tallafin man fetur, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki.
A cewar NERC, Gwamnatin Tarayya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 1.94 a matsayin tallafin farashin wutar lantarki a 2024 don cike gibin dake tsakanin ainihin farashin da ya kamata a biya da kuma farashin da aka amince da shi ga masu amfani.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta biya Naira miliyan 371.34 ne kaɗai daga cikin Naira tiriliyan 1.94 da take da alhakin biya, wanda ke wakiltar kashi 0.019 cikin ɗari kacal na biyan bashin tallafin.
Haka ne yasa a kwanakin baya ministan lantarki, ya bayyana cewa gwamnati na duba cire tallafin wutar.