Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban bankin aikin gona 

0
15
Tinubu
Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, a matsayin shugaban Bankin Cigaban Aikin Gona da aka sauyawa fasali.

Sanarwar naɗin ta fito ne a ranar Juma’a, tare da naɗin wasu mutum bakwai da za su jagoranci wasu manyan hukumomin gwamnatin tarayya daban-daban.

Muhammad Babangida, wanda ke da shekaru 53, ya samu digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci da kuma Hulɗar Jama’a daga Jami’ar Montreux, Switzerland. Haka kuma, ya kammala wani shirin horo a kan shugabanci da tafiyar da kamfanoni a makarantar koyar da harkokin kasuwanci ta Harvard Business School a shekarar 2002.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here