Gwamnatin Tarayya Tayi Gargadin Ambaliya a Jihohi 11, Ciki Har da Kano

0
33

Gwamnatin tarayya ta fitar da gargadin gaggawa kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wasu jihohi 11, ciki har da Kano, Akwa Ibom, Adamawa, da Borno. 

Wannan gargadi ya shafi daga 16 zuwa 20 ga watan Yuli, kamar yadda wata sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta nuna.

Sanarwar, wacce Ma’aikatar Muhalli ta tarayya ta fitar, ta samu sa hannun Daraktan cibiyar gargaɗi akan ambaliyar ruwa wato Usman Bokani.

Jihohin da ake hasashen za su iya fuskantar ambaliya sun haɗa da,

Adamawa: Mubi

Akwa Ibom: Edor, Upenekang, Oron, Eket

Borno: Ngala, Maiduguri

Bauchi: Azare, Bauchi, Itas, Jama’are, Kafin-Madaki, Jama’a, Kari, Misau

Cross River: Calabar, Akpap

Jigawa: Miga, Gwaram, Diginsa, Ringim, Dutse

Katsina: Daura

Kano: Kunchi, Kwaryar Kano, Gezawa, Wudil, Bebeji, Sumaila, Tudun Wada

Plateau: Jos, Bukuru, Mangu

Yobe: Jakusko, Machina, Dapchi

Zamfara: Bungudu, Gusau

Bokani ya bukaci hukumomin jihohi da masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan da suka dace domin rage illar da ambaliya ka iya haifarwa.

A baya, tsakanin watan Maris zuwa Yuni 2025, ambaliya, gurɓatar iska, da ruwan sama sun hallaka fiye da mutane 200 tare da raba sama da mutane 8,000 da muhallansu a jihohin Sokoto, Neja, Kaduna, Taraba, Ekiti, Ogun, Imo da wasu jihohi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here