Gwamnatin Jigawa Za Ta Fara Samar da Magunguna a jihar

0
14

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana shirin fara samar da magunguna a kamfanin JIPHARMA, wanda ke karkashin mallakin jihar, a wani yunkuri na habaka fannin kiwon lafiya.

Babban Manajan Kamfanin, Nasiru Alhassan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a garin Dutse, yayin da yake gabatar da rahoton ayyukan kamfanin na tsawon shekaru biyu da suka gabata karkashin gwamnatin Gwamna Umar Namadi.

Alhassan ya ce kamfanin na shirin fara samar da muhimman magunguna da ake yawan bukata kamar su Vitamin C, Paracetamol, da magungunan ruwa.

Ya kara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen saukaka samun magunguna a jihar, da kuma bunkasa harkar kiwon lafiya baki É—aya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here