Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a matsayin gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin a yau Juma’a, inda ya ce rasuwar Ɗantata ta girgiza shi matuƙa.
“Rasuwarsa ta matuƙar taɓa zuciyata. Wannan ne ya sa na zo da kaina domin na mika ta’aziyya bisa wannan babban rashi,” in ji shugaban ƙasa.
Ɗantata ya rasu ne a Dubai ranar Talata, 15 ga watan Yuli, 2025, sannan aka yi jana’izarsa a birnin Madina dake mai tsarki.
Shugaba Tinubu ya tuna yadda ya ziyarci marigayin a gidansa a lokacin yaƙin neman zaɓe na 2023 domin neman albarka. Ya ce duk da ya yi niyyar komawa domin gode masa bayan nasara, sai kuwa marigayin ne ya kawo masa ziyara a Abuja. “Wannan ya nuna irin sauƙin kai da halin kirki da ya ke da shi,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa Ɗantata ya kasance mutum mai son taimakawa, inda ya ce, “da taimako yana tafiya da mutum lahira, da yanzu za ku same shi a kasuwa yana raba abinci ga mabukata ko kuma yana ɗaukar nauyin magani ga marasa lafiya.”
Shugaban ya miƙa ta’aziyarsa ga iyalan marigayin, gwamnatin jihar Kano da daukacin al’ummar Najeriya, yana mai addu’ar Allah ya jikan Ɗantata, ya gafarta masa, ya kuma sa aljanna ta zama makomarsa.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna godiya bisa wannan ziyara da Shugaban ƙasa ya kawo domin jajantawa al’ummar jihar bisa wannan babban rashi.