Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai jagoranci wani taron addu’o’i na musamman domin karrama tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, a babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar da ma’aikatar yaɗa labarai ta ƙasa ta fitar ta bayyana cewa za a gudanar da taron ne da misalin ƙarfe biyar na yamma, inda manyan jami’an gwamnati da ministocin tarayya za su halarta.
Baya ga haka, taron zai kuma samu halartar shugabannin majalisun dokoki da kuma wakilai daga ɓangaren shari’a.
Wannan addu’a ta musamman na zuwa ne bayan gudanar da addu’o’in kwana uku a Daura, jiharsa ta haihuwa, a gaban tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa za a ci gaba da gudanar da addu’o’i na musamman a ranar Juma’a, a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.