Sojoji Sun Ki Karɓar Cin Hanci Naira Miliyan 13.7 daga ‘Yan Ta’adda 

0
10
Sojoji
Sojoji

Shalkwatar Tsaron ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun Operation Safe Haven sun ƙi karɓar cin hanci na Naira miliyan 13.7 da wasu ‘yan ta’adda suka yi ƙoƙarin ba su yayin wani aiki a kan hanyar Jos zuwa Sanga da ke Jihar Filato.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis, inda yayi bayani akan ayyukan tsaro da sojoji ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Kangye ya ce dakarun sun samu kiran gaggawa dangane da ayyukan ta’addanci a yankin, inda suka yi nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda biyu da suka yi ƙoƙarin ba su cin hanci da kudin Naira miliyan 13.7 domin su kubuta.

Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma gudanar da wasu hare-hare da kuma amsa kiran gaggawa a ƙananan hukumomin Bassa, Barkin Ladi, Wase, Riyom da Jos ta Gabas Jihar Filato.

A cewarsa, dakarun sun kai farmaki a ƙananan hukumomin Kaura da Sanga na Jihar Kaduna.

A cikin waɗannan hare-haren, dakarun sun gwabza da ‘yan bindiga, inda suka kashe wasu daga cikinsu, suka kama mutane 12 da ake zargi da hannu a ta’addanci, tare da ceto mutane uku da aka sace.

An kuma kwato bindigu, harsasai, babura da motoci daga hannun ‘yan ta’addan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here