Gwamnatin Jihar Kano tana shirin karɓar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a ranar Jumma’a 18 ga Yuli, 2025, domin ta’aziyya ga gwamnatin jihar da al’ummar Kano, tare da iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata.
Sanarwar hakan na ƙunshe cikin wata takarda da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan ziyara a matsayin alamar haɗin kan ƙasa da girmamawa ga al’ummar Kano da tarihin marigayi Alhaji Aminu Alasan Dantata.
Ya kuma yi kira ga jama’ar Kano da su tarbi Shugaban Ƙasa cikin mutunci da al’adun girmama baki da jihar ke da su.