Rashin wajen saukar jirgi ne ya hana ni zuwa jana’izar Buhari—Akpabio

0
7

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin samun wurin da jirginsu zai sauka a filin jirgin sama na Katsina ce ta hana shi halartar jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Akpabio, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ya ce, jiya, direban jirginmu ya yi iyakar ƙoƙarinsa don samun damar sauka a filin jirgin sama na Katsina, amma saboda yawan jirage da rashin isasshen wurin da jirgin mu zai sauka, dole muka dawo Abuja. 

Shugaban majalisar ya ce a ranar Laraba, ya samu rakiyar wasu Sanatoci zuwa gidan marigayin a Daura, inda suka gabatar da ta’aziyya ga iyalansa.

“Mun yi addu’ar neman gafarar Allah ga Buhari, tare da jajantawa uwargidansa, ’ya’yansa da ’yan uwa da abokan arziki,” in ji shi.

Akpabio ya ƙara da cewa sun kuma kai ziyarar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, sannan daga bisani suka gana da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, inda suka mika masa sakon ta’aziyyar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here